Isa ga babban shafi

Tyson Fury ya bukaci Anthony Joshua ya sa hannu a yarjejeniyar dambacewarsu

Tyson Fury ya sake kira ga Anthony Joshua da ya “bai wa masoya damben boxing abin da su ke so” ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar fafatawar da ya nemi su yi ta ajin masu nauyi a watan Disamba.

Anthony Joshua dan Birtaniya, yanzu haka bashi da kambu ko guda a hannunsa.
Anthony Joshua dan Birtaniya, yanzu haka bashi da kambu ko guda a hannunsa. © Andrew Couldridge et Isaac Brekken / AP Photo / Montage RFI
Talla

A makon da ya gabata ne dai, Zakaran WBC, Fury, mai shekaru 34, ya bai wa takwaransa Joshua, mai shekaru 32, wa'adin sa hannu a ranar Litinin, amma daga bisani ya ce ya tsawaita wa'adin zuwa ranar Alhamis.

Sai dai a yayin da ya ke mayar da martani kan batun mai magana da yawun Joshua Eddie Hearn ya ce "ya yi mamakin bukatar da Fury ke gabatar musu, la’akari da cewar ba shi da tsayayyar magana.

A cewar Hearn cikin kiftawar idanu zaka iya jin Tyson Fury ya ce yana bukatar dambacewa da kai, nan da nan kuma sai ya ce ya fasa, tare da kokarin taro wani na dabam.

Tuni dai tawagar Joshua ta amince da tayin da Fury ya yi na karawar da za su yi, da kuma raba kudaden da za a biya zuwa kashi 60 da 40, bayan fafatawar da za su yi a ranar 3 ga watan Disamba.

A watan da ya gabata, Joshua ya kasa kwato kambunsa guda uku na WBA, da WBO da IBF a karawar da suka yi da Oleksandr Usyk dan kasar Ukraine, inda ya sha kashi bayan tantance makin da kowannensu ya samu a tsawon turamen da suka kece reini a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.