Isa ga babban shafi

Tyson Fury ya janye batun dambacewa da Antony Joshua

Tyson Fury ya bayyana cewa ba zai fafata damben boxing da Anthony Joshua ba, saboda rashin sanya hannu a kwangilar karawar da za su yi.

Anthony Joshua da Tyson Fury.
Anthony Joshua da Tyson Fury. © Andrew Couldridge et Isaac Brekken / AP Photo / Montage RFI
Talla

Fury ya dauki matakin ne bayan karewar wa’adin da ya baiwa Joshua na zuwa karfe 5 na yammacin jiya litinin dangane da sa hannun da ya kamata yayi akan kulla yarjejeniyar dambacewar da aka yi fatan ganin  sun yi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Joshua ya ce zai rattaba hannu kan kwantiragin karawa da Fury bayan wa’adin da zakaran damben boxing na WBC ya bayar .

Yayin da ya ke kare kansa kan batun, Anthony Joshua ya ce rattaba hannu akan yarjejeniyar kece raini da Tyson Fury ba hakkinsa bane, sai dai fa lauyoyins, kamar yadda doka ta tanada.

To a halin da ake ciki dai Fury na iya fafatawada wani a damben boxing kafin karshen shekara, amma karawar da ake dakon ganin yayi da Oleksander Usyk mai rike da kambun WBO, WBA da IBF sai zuwa cikin sabuwar shekara ta 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.