Isa ga babban shafi

Joshua ya karbi kalubale don dambacewa da Fury a karshen shekara

Zakaran damben boxin na duniya ajin masu nauyi, Tyson Fury ya bai wa Anthony Joshua damar fadan neman kambun damben duniya a karshen wannan shekarar.

Anthony Joshua da Tyson Fury.
Anthony Joshua da Tyson Fury. © Andrew Couldridge et Isaac Brekken / AP Photo / Montage RFI
Talla

Fury, mai shekaru 34, ya na neman wanda za su fafata da shi bayan da abokin hamayyarsa Oleksandr Usyk, ya nuna cewa ba zai koma fagen dambe ba har sai zuwa shekarar 2023.

Joshua dan Najeriya, wanda Usyk dan kasar Ukraine, ya doke shi a Saudi Arabia cikin watan da ya gabata, ya karbi kalubalen Fury, ya na mai cewa watan Disamba ya yi mai dai dai.

Fury ya shaida wa Joshua cewa, ya na sane da cewa bashi da kambu ko guda 1 yanzu haka a hannunsa bayan doke shi a watan jiya, dalili kenan da ya kalubalance shi kan fadan don ya zama dama gareshi ta samun sabon kambu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.