Anthony Joshua ya koma na 5 a jerin fitattun ‘yan damben duniya
Tsohon zakaran damben boxin ajin masu nauyi na WBA, dan asalin Najeriya dake Birtaniya Anthony Joshua, ya koma matsayi na biyar a jerin fitattun ‘yan damben duniya na baya-bayan nan.
Wallafawa ranar:
A watan Satumban shekarar nan ta 2021, Joshua ya rasa damararsa ta ban girma a hannun Oleksandr Usyk bayan kayen da ya sha a fafatawar da suka yi.
Sai dai Joshua na shirin sake karawa da Usyk dan kasar Ukraine a cikin shekarar 2022 dake tafe.
Masu sharhi dai na alakanta raguwar darajar Joshua a ajin masu nauyi na ‘yan damben duniya da mummunan kayen da ya sha a hannun Usyk.
Sabon jadawalin darajar ‘yan damben boxin din na duniya dai ya nuna a halin yanzu Daniel Dubois dan Birtaniya ne ke matsayi na daya, yayin da Michael Hunter dan Amurka ya kasance a matsayi na biyu.
Robert Helenius da Hughie Fury ne a matsayi na uku da na hudu, yayin da Deontay Wilder, wanda ya rasa kambunsa a hannun Tyson Fury, ke matsayi na shida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu