Isa ga babban shafi
Wasanni

Joshua ya ci gaba da rike kambin duniya bayan doke Kubrat Pulev

Anthony Joshua ya ci gaba da rike kambin duniya ajin nauyi na damben zamani, bayan doke Kubrat Pulev, a karan-batta da zaratan ‘yan damben Boxing din sukayi a birnin London.

Anthony Joshua ya ci gaba da rike kambin duniya ajin nauyi na damben zamani, bayan doke Kubrat Pulev, a karan-batta da zaratan ‘yan damben Boxing din sukayi a birnin London.
Anthony Joshua ya ci gaba da rike kambin duniya ajin nauyi na damben zamani, bayan doke Kubrat Pulev, a karan-batta da zaratan ‘yan damben Boxing din sukayi a birnin London. pool via REUTERS/Andrew Couldridge
Talla

Sau biyu ake dage fafatawa tsakanin jaruman guda biyu saboda raunin da Pulev na Bulgaria ya samu a kafadarsa da kuma batun annobar coronavirus.

Joshua na Birtaniya amma dan asalin Najeriya ya kare kambunsa na IBF da WBA da WBO a filin wasa na Wembley kuma a gaban ‘yan kallo kimanin dubu 1 da aka takaita yawansu saboda annobar coronavirus.

Bayan nasarar da Anthony Joshua ya samu, magoya bayansa sunyi ta ihu suna cewa 'saura Fury', inda gwanin nasu ya amsa da cewa 'duk wanda ke da tarin kofuna ya tinkare shi, ciki harda Tyson Fury.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.