Isa ga babban shafi
Wasanni

Joshua zai kare kambinsa a karawarsa da Pulev

A wannan Asabar ake karan-batta tsakanin zaratan ‘yan damben Boxing wato Anthony Joshua da Kubrat Pulev a birnin London.

Anthony Joshua da Kubrat Pulev
Anthony Joshua da Kubrat Pulev talksport
Talla

Sau biyu aka dage fafatawa tsakanin jaruman guda biyu saboda raunin da Pulev na Bulgaria ya samu a kafadarsa da kuma annobar coronavirus.

Yanzu haka Joshua na Birtaniya amma dan asalin Najeriya zai kare kambunsa na IBF da WBA da WBO a ranar Asabar a filin wasa na Wembley kuma a gaban ‘yan kallo kimanin dubu 100 da aka takaita yawansu saboda annobar coronavirus.

Raban da Joshua ya fafata da wani dan dambe, tun lokacin da ya doke Andy Ruiz a Saudiya watanni 12 da suka gabata, wasan da ya ba shi damar karbe kambun WBA da WBO da IBF.

Dan wasan ya ce a shirye yake ya sha dukkanin naushe-naushe har matakin karshe na fafatawarsa da Pulev.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.