Isa ga babban shafi
Wasanni

Joshua zai yi dambensa na gaba a Tottenham

Zakaran damben Boxing Anthony Joshua ya zabi filin wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham don dambacewa a karawarsa ta watan Yuni, a kokarinsa na kare kambunsa bayan nasara kan Andy Ruiz Junior cikin watan Disamba a Saudiya.

Anthony Joshua zakaran damben Boxing na duniya.
Anthony Joshua zakaran damben Boxing na duniya. Andrew Couldridge/Reuters
Talla

Jaridar wasanni ta Sky ta ruwaito Eddie Hearn guda cikin masu shirya wasanni a Birtaniya na cewa, Joshua ya samu gayyata daga kasashen Amurka da yankin gabas ta tsakiya har ma da Africa baya ga Turkiya amma dan damben yafi kaunar gudanar da wasan nashi a London.

A baya dai Joshua mai shekaru 30 ya ce ya yi fatan akwai wadataccen lantarki kuma dawwamamme a mahaifarshi Najeriya da babu abin da zai hana shi doka wasan na shi a can.

Karawar ta Joshua cikin watan Yuni dai za ta kasance tsakaninshi da Kubrat Pulev dan Bulgaria wasan da zai kasance mai cike da kalubale ga Joshua.

Rabon Joshua ta doka wasan a gida dai tun cikin watan Satumban 2018 da ya yi nasara kan Alexander Povetkin a filin wasa na Wembley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.