Isa ga babban shafi
Wasanni

Joshua ya kare kambun dambensa hudu a lokaci guda

Gwarzon dan damben boxing na duniya ajin masu nauyi na Birtaniya Anthony Joshua, ya kare kambunsa guda hudu a lokaci guda, da suka hada da IBF, IBO WBO da kuma WBA, bayan fafatawar da yayi da Alexander Povetkin na Rasha.

Anthony Joshua, yayin lallasa Alexander Povetkin, yayin fafatawar da suka yi a ranar 22 ga Satumba, 2018, a filin wasa na.
Anthony Joshua, yayin lallasa Alexander Povetkin, yayin fafatawar da suka yi a ranar 22 ga Satumba, 2018, a filin wasa na. Andrew Coulridge/Reuters
Talla

A ranar Asabar da ta gabata ne, Joshua ya kece raini da Povetkin a filin wasa na Wembley da ke birnin London.

Anthony Joshua wanda iyayensa ‘yan asalin garin Sagamu ne dake jihar Ogun, ya samu nasarar buge Povetkin ne bayan fafatawa tsawon turmi ko zagaye 7.

Kimanin ‘yan kallo dubu 80, 000 ne suka shaida fafatawar zaratan ‘yan damben biyu a Wembley, wanda bayan kammalawa ya tabbata cewa Joshua da ya zama zakara zai karbe kyautar fam miliyan 20, yayinda Povetkin da ya sha kaye, zai samu kyautar fam miliyan 6.

A halin yanzu Joshua dan asalin Najeriya zai jira wanda zai yi nasara a fafatawar da za a yi tsakanin Tyson Fury na Birtaniya da Deontay Wilder na Amurka a watan Disamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.