Isa ga babban shafi
Wasanni

Zan doke Joshua tun a zagaye na biyu - Fury

Tyson Fury ya yi ikirarin cewa zai doke zakaran damben Boxing ajin nauyi Anthony Joshua tun a zagaye na biyu a fafatawar da suke shirin yi, saboda a cewarsa yanayin kwari da yake ji kwanan nan.

Antony Joshua da Tyson Fury
Antony Joshua da Tyson Fury Skysport
Talla

Fury mai rike da kambin WBC ya ce biyo bayan fafatawa biyu da Joshua ya yi da suka bashi nasara a kan Andy Ruiz Junior a watan Disambar 2019 da kuma zagaye har na tara kafin doke Kubrat Pulev a watan da ya gabata, yace Joshua bazai kai labari a kansa ba.

Dama dai fafatawar da ake jira kenan, tun bayan nasarar da Anthony Joshua ya samu a karawar karshe da yayi da Kubrat Pulev a watan Disemba.

Yanzu haka Anthony Joshua shi ke rike da kambin duniya ajin nauyi na damben zamani, bayan doke Kubrat Pulev, a karan-batta da zaratan ‘yan damben Boxing din sukayi a birnin London.

Joshua na Birtaniya amma dan asalin Najeriya ya kare kambunsa na IBF da WBA da WBO a filin wasa na Wembley kuma a gaban ‘yan kallo kimanin dubu 1 da aka takaita yawansu saboda annobar coronavirus.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.