Isa ga babban shafi
Wasanni - Dambe

Joshua ya musanta karbar cin hancin fam miliyan 15 don fasa karawa da Usyk

Fitaccen dan damben boxing ajin masu nauyi Anthony Joshua dan Ingila, ya yi watsi da rahotannin cewa ya amince da yarjejeniyar karbar fam miliyan 15 kwatankwacin Yuro miliyan 18 don janyewa daga shirin sake karawa da Oleksandr Usyk na kasar Ukraine.

Oleksandr Usyk bayan narkawa Anthony Joshua naushi yayin karawar da suka yi a watan satumban shekarar 2021.
Oleksandr Usyk bayan narkawa Anthony Joshua naushi yayin karawar da suka yi a watan satumban shekarar 2021. Adrian DENNIS AFP
Talla

A watan Satumban shekarar bara ne dai Usyk ya kwace dukkanin kambun Joshua na WBA da IBF da kuma WBO, bayan lallasa Joshuan da yayi a fafatawar da suka yi.

Rashin nasarar da Joshua ya yi a karon battarsa da Oleksandr Usyk, itace karo na biyu da fitaccen dan damben boxing din ya fuskanta tun bayan ficen da yayi.

A baya bayan nan ne kuma kafafen yada labarai da dama ciki har da na kasar Birtaniya suka wallafa rahoton cewa, Joshua ya yarda Usyk ya biya fam miliyan 15, domin janyewa da shirin sake fafatawar da aka tsar za su yi, labarin da fitaccen dan damben dan asalin Najeriya ya bayyana a matsayin mara tushe.

A karshen watan Satumban da ya gabata, fitaccen dan damben boxing na Ingila ya kafe kan cewa zai iya fafatawa da Tyson Fury wani fitaccen dan damben na boxing wani lokaci nan gaba kadan, koda kuwa ba tare da kambunansa guda uku na duniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.