Isa ga babban shafi
Wasanni - Dambe

Joshua bai daddara da dukan da ya sha a hannun Usyk ba

Fitaccen dan damben boxing na Ingila dan asalin Najeriya, Anthony Joshua ya kafe kan cewa zai iya fafatawa da Tyson Fury wani fitaccen dan damben na boxing wani lokaci nan gaba kadan, koda kuwa ba tare da kambunansa guda uku na duniya ba.

Oleksandr Usyk, a daidai lokacin da ya dirka wa Anthony Joshua wawan naushi, yayin fafatawar damben boxing a filin wasa na kungiyar Tottenham.
Oleksandr Usyk, a daidai lokacin da ya dirka wa Anthony Joshua wawan naushi, yayin fafatawar damben boxing a filin wasa na kungiyar Tottenham. Adrian DENNIS AFP
Talla

A ranar Asabar din da ta gabata, Joshua ya rasa kambunsa na zakaran damben boxing na duniya ajin masu nauyi da suka hada da WBA, IBF da kuma WBO, bayan kayen da ya sha a fafatawar da yayi da Oleksandr Usyk a filin wasa na kungiyar Tottenham Hotspur.

Anthony Joshua bayan shan kaye a karawar sa da Oleksandr Usyk.
Anthony Joshua bayan shan kaye a karawar sa da Oleksandr Usyk. Adrian DENNIS AFP

Sai dai tuni wakilan Anthony Joshua suka tabbatar da cewa zai sake fafatawa da Usyk domin kwato kambunsa guda 3, yayin da shi kuma Joshua ke jin har yanzu yana karawa da Tyson Fury ko da ba tare da lambobinsa na duniya ba.

Rashin nasarar da Joshua ya yi a karon battarsa da Oleksandr Usyk a ranar Asabar, itace karo na biyu da fitaccen dan damben boxing din ya fuskanta tun bayan ficen da yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.