Isa ga babban shafi

Anthony Joshua ya koma na 6 a jerin 'yan dambe ajin masu nauyi na WBC

Zakaran damben boxing na duniya har sau biyu Anthony Joshua ya zama na shida cikin jerin ajin WBC na ‘yan damben masu nauyi gabanin fafatawar da zai yi da zakara Tyson Fury.

Anthony Joshua na shirin karawa da Tyson Fury a wasa na gaba.
Anthony Joshua na shirin karawa da Tyson Fury a wasa na gaba. AFP
Talla

Dan Birtaniyar wanda asalinsa dan Najeriya ne ya koma lamba na 6 a duniya ne  biyo bayan kayen da ya sha har sau biyu a jere, a hannun Oleksandr Usyk, wanda a yanzu ke cigaba da rike da kambun damben boxing ajin masu nauyi na WBA, IBF da WBO, bayan sake karawar da suka yi a Saudiyya cikin Agusta

Fury, wanda ya lallasa Dillian Whyte a Wembley cikin watan Afrilu, ya fara takalar Usyk domin su kara, amma dan Ukraine din ya ce ba zai sake fafata dambe ba har zuwa cikin shekarar 2023.

Tun daga lokacin ne Fury ya shiga kafafen sada zumunta inda ya yiwa Joshua tayin su kara.

A ranar Talata kuma tawagar Joshua ta tabbatar da cewa ta amince da sharuddan da takwararta ta Fury ta gindaya gabanin fafatawar da za su yi a ranar 3 ga watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.