Isa ga babban shafi

Anthony Joshua ya amince da fita daga gasar zakarun boxing na Duniya

Anthony Joshua ya amince cewa ya fita daga gasar zakarun ‘yan damben boxing na duniya, domin mayar da hankali kan sake shirin tunkarar kalubalen da ke gabansa.

Anthony Joshua dan damben Birtaniya.
Anthony Joshua dan damben Birtaniya. Andrew Couldridge/Reuters
Talla

Joshua ya yi fafatawa ta karshe a cikin watan Agusta, inda ya sha kashi a Hannun Oleksander Usyk, karo na biyu a jere abinda ya say a kasa kwato kambunsa na WBA, WBO, IBF da IBO.

Daga baya Tyson Fury ya yi wa Joshua tayin su kara akan kambun WBC, amma ‘yann kasar Birtaniyar suka kasa cimma matsaya kan yiwuwar fafatawar damben ta ajin masu nauyi.

A halin yanzu dai an alakanta Joshua, mai shekaru 33, da yiwuwar sake karawa da Dillian Whyte, wanda shi Joshuan ya taba shank aye yayin karawarsu a lokacin da ke bako a fagen Damben na Boxing, sai dai a shekarar 2015 ya dauki fansar doke shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.