Isa ga babban shafi

Joshua ya ce lokaci ya yi da ya kamata su dambace da Tyson

Shahararren dan damben boksin na kasar   Ingila, dan asalin Najeriya, Anthony Joshua ya kalubalanci takwaransa Tyson Fury, inda ya ce yanzu ne lokacin da ya dace su gwada kwanji ta wurin gwabza dambe.

Anthony Joshua ya gayyaci Tyson Fury don su dambace.
Anthony Joshua ya gayyaci Tyson Fury don su dambace. AFP
Talla

Tattaunawa tsakanin Oleksandr Usyk, da Fury a kan yiwuwar fafatawa ta wargaje a makon da ya gabata.

Joshua, mai shekaru 33, zai dambace ne da takwaransa na Amurka, Jermaine Franklin a ranar Asabar, wasansa na farko a cikin wannan shekarar Kenan.

Ya ce babu wani lokaci da ya fi dacewa  su shiga filin daga da Fury face yanzu, domin debe takaicin wargajewar wancan  tattaunawa.

A shekarar da ta gabata, Joshua ya tattauna da  Fury a kan dambacewa, amma suka gaza cimma matsaya, saboda haka Fury ya dambace da Derek Chisora a filin wasa na  Wembley a watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.