Isa ga babban shafi

Adesanya na fuskantar barazanar daurin watanni uku da kuma biyan tara

Tsohon zakaran damben UFC ajin masu matsakaicin nauyi Israel Adesanya, na fuskantar barazanar shafe wata uku a gidan yari da kuma biyan tarar dala dubu biyu, sakamakon kama shi da laifin tuki bayan ya sha barasa a New Zealand.

Fitaccen dan wasan dambe Adesanya
Fitaccen dan wasan dambe Adesanya Getty Images via AFP - HARRY HOW
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Agustan da ya gabata, kafin rashin nasarar da ya yi ta baya-bayan nan.

Dan wasan haifaffen Najeriya na kan hanyarsa ta komawa gida ne bayan halartar wata liyafar cin abinci da abokansa suka shirya a birnin Auckland, kuma nan take ya yi karo da wani shingen daukar marasa lafiya.

An samu Adesanya da miligram 87 na barasa a jininsa, abinda ya wuce adadin dokar da kasar ta baiwa mutum damar sha na miligrama 50 kowacce rana.

Tuni dai Adesanya ya amsa laifinsa, inda ya nemi afuwar magoya baya da masoya, ya na mai cewa duk da ya san bai kamata ya yi tuki  a lokacin da ya cikin barasa ba, amma dai tsautsayi ne ya afka masa.

Ta cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter, Adesanya ya ce sam bai kamata ya aikata hakan ba, don haka zai amshi kowanne irin hukunci aka yanke masa  da hannu bibbiyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.