Sama da bakin haure 40 sun bace bayan kifewar kwale-kwalensu a ruwan Italiya
Majalisar Dinkin Duniya tace, sama da mutane 40 ne suka bace bayan da wani kwale-kwalen bakin haure ya kife a tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.
Wallafawa ranar:
Wakilin Hukumar kula da ‘yan gudun hijara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR a Italiya Chiara Cardoletti tace tun ranar Alhamis ne kwale-kwalen ya kife kuma tace wani jariri aka haifa na cikin wadanda suka bata, Jirgin ruwan ya taso ne daga Sfax na kasar Tunisiya kuma yana dauke da bakin haure 46 daga kasashen Kamaru da Burkina Faso da Ivory Coast.
Flavio Di Giacomo, kakakin hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya IOM, yace Kwale-kwalen ya kife ne saboda iska mai karfi da igiyar ruwa, inda aka kai wasu da suka tsira zuwa Lampedusa, wasu kuma an dawo da dasu Tunisia.
Tsibirin Lampedusa na kudancin Italiya na da tazarar kilomita 145 daga gabar tekun Tunisiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu