Isa ga babban shafi

Sama da bakin haure 70 ake fargabar sun bace a gabar ruwan Girka

Akalla mutane 78 ne suka mutu inda ake fargabar da dama sun bace, bayan da wani karamin jirgin ruwa dauke da bakin haure ya kife a ruwa a kasar Girka, hatsari mafi muni da ya auku a wannan shekara in ji MDD.

Wasu bakin haure da suka isa gabar ruwan Girka daga Turkiyya kenan.
Wasu bakin haure da suka isa gabar ruwan Girka daga Turkiyya kenan. © AP Photo/Emrah Gurel
Talla

Kwale-kwalen wanda ya nutse a kudancin gabar tekun Girka, mai nisan kilomita 87 daga kudu maso yammacin Pylos, hukumomi sun ce masu aikin ceto sun fuskanci kalubale sakamakon kakkafar iska da ta kunno kai.

Yanzu haka dai kusan mutum 100 aka samu nasarar cetowa, inda ake ci gaba da laluben wadanda suka bata.

An dai yi amfani da jirage masu saukar Angulu wajen ceto mutanen, kuma sojojin saman a ci gaba da lalube.

Tuni aka mika mutum hudud aga cikin wadanda aka ceto zuwa asibitin birnin Kalamata, sakamakon cewa jininsu ya sauka, wanda likitoci ke fargabar cewa rayuwarsu na cikin hatsari.

An dai mika gomman wadanda suke da lafiya zuwa sansanonin da aka ware musu, domin basu kayayyakin sawa, kamar yadda MDD ta tanadar musu.

Har yanzu dai babu cikakken bayan kan adadin mutanen da suka makale a ruwa, amma dai rahotanni na cewa adadin bakin hauren da suka fito daga kasashen Masar, Syria da kuma Pakistan ya haura 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.