Isa ga babban shafi

Bakin Haure: Har yanzu an gaza cimma jituwa tsakanin Faransa da Italiya

Ministan harkokin wajen Italiya ya soke ziyarar da zai kai birnin Paris, bayan da ministan cikin gida na Faransa ya soki manufofin da suka shafi bakin haure na gwamnatin Rome, a wani sabon cece-ku-ce game da takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, Firaministan Italiya Giorgia Meloni, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Firayim Ministan Kanada Justin Trudeau, Shugaban Amurka Joe Biden, Firayim Ministan Burtaniya Rishi Sunak, Firaministan Spain Pedro Sanchez, Firayiministan Netherland Mark Rutte, Firayiministan Japan Fumio Kishida, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken da Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel lokacin da suka halarci taron gaggawa na shugabannin duniya bayan fashewar makami mai linzami na Rasha a Poland, a Bali, Indonesia, Nuwamba 16, 2022.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, Firaministan Italiya Giorgia Meloni, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Firayim Ministan Kanada Justin Trudeau, Shugaban Amurka Joe Biden, Firayim Ministan Burtaniya Rishi Sunak, Firaministan Spain Pedro Sanchez, Firayiministan Netherland Mark Rutte, Firayiministan Japan Fumio Kishida, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken da Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel lokacin da suka halarci taron gaggawa na shugabannin duniya bayan fashewar makami mai linzami na Rasha a Poland, a Bali, Indonesia, Nuwamba 16, 2022. REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

A wata hira da aka yi da shi ta gidan rediyo a birnin Paris, Gerald Darmanin ya ce firaministar Italiya Giorgia Meloni ta gaza wajen warware matsalolin bakin hauren da kasarta ke fuskanta.

Hakan ta sanya ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani yin tir da kalaman Darmanin yana cewa ba za su lamunta da irin wadannan kalamai ba, abin da ya fusata gwamnatin Italiya soke ziyarar da ya shirya zuwa birnin Paris.

Daga bisani gwamnatin Paris ta nemi a sassauta zaman dar-dar, inda ta ce tana fatan za a sake dage ganawar da aka shiryawa Tajani da takwararta ta Faransa Catherine Colonna.

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce gwamnatin kasar na son yin aiki tare da Italiya domin fuskantar kalubale da ke haddasa kwararar bakin haure cikin hanzari.

Gwamnatin Faransa mai matsakaicin ra'ayi karkashin shugaba Emmanuel Macron ta sha samun rashin jutuwa da majalisar ministocin Italiya a shekarun baya-bayan nan kan matsalolin da ssuka shafi bakin haure.

An samu rashin jituwa a watan Nuwamban da ya gabata tsakanin kasashen biyu, lokacin da Meloni, wanda jam'iyyarta ta masu ra'ayin rikau ta ki barin wani jirgin ruwan agaji dauke da bakin haure 230 ya tsaya a Italiya.

A karshe dai an bar jirgin ruwan Ocean Viking ya tsaya a Faransa, amma gwamnatin Paris ta yi Allah wadai da halin da Rome ta jefa ‘yan ciranin, tare da dakatar da shirin karbar bakin haure 3,500 daga Italiya.

Fiye da mutane 42,000 ne suka isa tun ranar 1 ga Janairu, a cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan Italiya, wanda ya ninka kusan sau hudu na adadin da aka samu a shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.