Isa ga babban shafi

Muna neman wasu kasashe su taimaka wa bakin haure 234 da suka makale - SOS

Kungiyar ceto bakin haure SOS Mediterranee ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Faransa, Girka da Spain da su taimaka wajen nemo tashar jiragen ruwa da za a ajiye mutane 234 da aka ceto a lokacin da suke kokarin isa Turai, bayan da Italiya da Malta suka kasa kai musu dauki.

Wasu bakin haure da suka makale a teku kenan
Wasu bakin haure da suka makale a teku kenan © Reuters
Talla

Kungiyar mai zaman kanta, wadda jirgin ruwanta na Ocean Viking ya bada agaji ga bakin haure da ke cikin kunci a tekun Bahar Rum, ta ce wannan ne karon farko da ta nemi agajin kai tsaye daga kasashen uku.

Tun bayan fara aikin nata na baya-bayan nan a ranar 22 ga watan Oktoba, kungiyar ta nemi kasashen Malta da Libya, kasar da galibin bakin haure da ke fatan isa Turai daga Afirka ke amfani da ita, da su ba su damar yada zango a tashoshinsu na jiragen ruwa, tunda su ne kasashe mafi kusa da wuraren da ake ceto.

Daga nan sai jirgin ya nemi agaji daga Italiya, wato inda sabuwar firaministar kasar Giorgia Meloni ta sha alwashin hana bakin haure tsallakawa Turai daga Afirka.

Ya zuwa ranar alhamis, ba ta samu wani martani a hukumance ba, amma kungiyar ta ce tana fuskantar haramcin shiga tashoshin jiragen ruwa na Italiya.

Tun daga farkon wannan shekara, bakin haure 1,765 ne suka mutu ko kuma suka bace a tsakiyar tekun Mediteriniya, lamarin da ya zama hanya mafi hadari, musamman ga mutanen da ke yin kaura a sassan duniya, a cewar hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.