Faransa ta karbi bakin da suka yi ta gararamba a teku
Bayan share tsawon kwanaki ana gararamba da su a kan teku cikin wani jirgin ruwan agaji mai suna Ocean Viking, a safiyar yau juma’a ‘yan ci-rani 230 sun sauka a tashar jiragen ruwan Toulon da ke kudancin Faransa.
Wallafawa ranar:
Jirgin ruwan wanda wata kungiyar agaji ta Faransa ke kula da ita, ta kwaso bakin hauren ne daga gabar ruwan Libya, kafin a dauki tsawon makwanni ana neman tashar jiragen ruwan da za ta karbe su.
Gabanin wannan lokaci dai, Faransa ba ta taba barin wani jirgin ruwa dauke da bakin haure daga Tekun Mediterranean sauka a gabarta ba, amma a wannan karon ta amince da haka saboda kasar Italiya ta ki karbar bakin.
Tuni Firaministan Italiya Giorgia Meloni ta soki gwamnatin Faransa kan yadda ta karbi bakin da ta ce Rome ta ki amincewa da su.
Tun da fari, gwamnatin Faransa ta ce, Italiya ce ke da alhakin karbar bakin amma ta yi biris, kuma wannan al'amari shi ne rikicin baya-bayan tsakanin kasashen biyu game da matsalar bakin haure da ke balaguro zuwa Turai daga nahiyar Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu