Isa ga babban shafi

Faransa ta bai wa Tunisia tallafin kudi don dakile kwararar bakin haure

Faransa ta bai wa Tunisia tallafin zunzututun kudi har sama Euro miliyan 25 domin taimaka mata yakar kwararar baki ba bisa ka’ida zuwa Turai. 

Wasu daga cikin bakin haure kan hanyarsu ta zuwa Turai.
Wasu daga cikin bakin haure kan hanyarsu ta zuwa Turai. AFP - FETHI BELAID
Talla

An sanar da wannan tallafi ne yayin ziyarar da Ministan Cikin Gidan Faransa Gérald Darmanin da takwaransa na Jamus Nancy Faeser suka kai birinin Tunis ranar Litinin, ziyarar da ta biyo ta shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai suka kai kasar bayan mummunar iftila’in da ya rutsa da bakin haure a mashigin ruwan Girka inda daruruwa suka bace. 

Ministan Cikin Gidan Faransan, Darmanin ya bayyana cewa,

Wannan tallafi ne da zai taimaka wajen samun kayayyakin aikin da ake buƙata da kuma shirya horo mai amfani, musamman ga 'yan sandan Tunisiya da masu tsaron kan iyaka, don dakile kwararar bakin-haure ba bisa ƙa'ida ba da maida su cikin yanayi mai kyau. 

Koda yake Ministan ya kara da cewa, kasashen Turai ba su da wani alhaki kan Tunisiya na samar musu da tsaron kan iyakoki, amma a cewarsa, dole ne su hubbasa don rage kwararar baki. 

"Wannan shi ne abin da Tunisiya ta nema don samun damar hana kwararar baki dake bin ruwa babu tsari." inji Darmanin.

Dimbin 'yan ci-rani ne ke rasa rayukansu akan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai domin samun ingantacciyar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.