Isa ga babban shafi

Tsohon Firaministan Italiya ya mutu bayan fama da jinya

Tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi, ya mutu yana da shekaru 86, bayan fama da rashin lafiya.

Tsohon Firaministan kasar Italiya Silvio Berlusconi
Tsohon Firaministan kasar Italiya Silvio Berlusconi AFP/File
Talla

Hamshakin attajirin da ya mallaki kafar watsa labarai ya mutu ne a asibitin San Rafaelle da ke birnin Milan.

Kafin mutuwarsa, Berlusconi ya jagoranci gwamnatocin Italiya daban daban tsawon fiye da shekaru 9.

Lokutan da marigayin ya jagorannci gwamnatocin kasar ta Italiya sun hada da shekarar 1994 zuwa 1995, sai kuma 2001 zuwa 2006, da kuma shekarar 2008 zuwa 2011.

Tun shekarar 2019 har zuwa lokacin mutuwarsa, Silivio Berlusconi ya ke zauren majalisar dokokin Italiya, mukamin da ya taba rikewa a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2001.

A watannin baya, tsohon Firaministan na Italiya ya sha fama da cutuka da dama, cikinsu kuma har da annobar  Korona a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.