Italiya
Kotu na gudanar da sabuwar shari'ar Berlusconi na Italiya
A wannan talata, kotu na sauraron shaidu a game da wata shari’ar da take yi wa tsohon Firaministan kasar Italiya Silvio Berlusconi, dangane da zargin rashawa.
Wallafawa ranar:
Talla
Kotun wadda ke zama a garin Naples, za ta saurari lauyoyinsa Berlusconi da za su wakilce shi a gabanta wato Michele Cerabona da kuma Niccolo Ghedini, inda a wannan karo ake zarginsa da bai wa wani dan Majalisar dattawan kasar rashawa domin taimaka masa kayar da gwamnatin Romano Prodi da ke kan karagar mulki a 2006.
Kotun dai za ta ci gaba da zama har zuwa gobe laraba, domin sauraron shaidu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu