Isa ga babban shafi
Italiya

An bukaci Kotu ta daure Berlusconi shekaru 5

Ma su Gabatar da kara a Italiya sun bukaci kotu ta daure tsohon Firaminista Silvio Berlusconi shekaru 5 a gidan yari saboda zargin cin hanci da rashawa. Wani jami’in kotun ya ce Alkali zai yanke hukunci kan shari’ar ranar 8 ga watan gobe kan tuhumar da ake yi wa Tsohon Shugaban na bai wa Dan Majalisar Dattawan kasar cin hanci don ya tsige gwamnati a shekarar 2006 zuwa 2008.

Tsohon Fimiyan Italiya Silvio Berlusconi
Tsohon Fimiyan Italiya Silvio Berlusconi REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Masu gabatar da kara sun kuma bukaci daure Valter Lavitola wani na hannun daman Berlusconi shekaru 4 da wata 4 saboda biyan kudin cin hancin yuro miliyan 300 ga Sanata Sergio De Gregorio don ficewa daga gwamnatin Romano Prodi.

Sai dai kuma a tsarin dokar Italiya yana da wahala Berlusconi ya je kidan kaso saboda shekarunsa na haihuwa 78.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.