Isa ga babban shafi
Italiya

Kotun Italiya ta wanke Berlusconi daga zargin lalata

Wata kotun kasar Italiya, a yau Juma’a ta wanke tsohon Firaministan kasar Silvio Berlusconi daga zargin da ake ma sa na yin lalata da wata karamar yarinya. Mai shari’a Enrico Tranfa ne ya wanke attajirin bayan ya yi watsi da bukatar masu shigar da kara da suka nemi a yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.

Tsohon Firaministan Italia, Silvio Berlusconi
Tsohon Firaministan Italia, Silvio Berlusconi REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

An zargi Berlusconi ne da yin lalata da wata Yarinya mai suna Karima Mahroug ‘yar rawa mai shekaru 17 na haihuwa.

Berlusconi ya dade yana fuskantar tuhume tuhume tun a shekara ta 1980, yawanci akan zargin rashawa ko wata badakalar kudi da ta shafi kasuwancinsa.

Yanzu haka tsohon Firaministan yana aikin hidima ga al’umma a wata cibiyar kula da lafiyar masu tabin hankali a kusa da Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.