Isa ga babban shafi

NATO ta fara wani atisayen Sojin sama mafi girma a Jamus

Kungiyar tsaro ta NATO ta fara wani gagarumin atisayen Sojin sama a Jamus irinsa mafi girma da kungiyar ta taba jagoranta a cikin Turai a wani yunkuri na kange barazanar Rasha ga tsaron nahiyar.

Jiragen yakin Sojin kungiyar tsaro ta NATO.
Jiragen yakin Sojin kungiyar tsaro ta NATO. AFP - KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Atisayen Sojin na NATO na zuwa ne a dai dai lokacin da Ukraine ke sake kwato wasu yankunanta da Rasha ta mamaye a yankin kudu maso gabashin kasar sakamakon wasu jerin hare-hare da dakarunta ke kaiwa.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla jirage 250 daga kasashen kungiyar 25 da kuma kawayensu da suka kunshi Japan da kuma Sweden da ke fatan shiga kungiyar ne za su gudanar da atisayen nay au litinin da za a shafe kwanaki 3 ana yi.

Fiye da dakarun Soji dubu 10 ne za su yi atisayen na yau litinin wadanda za su yi musayar dabaru kan kariya daga hare-haren jirage marasa matuki da kuma makamai masu linzami na ruwa a wani yunkuri na bayar da kariya daga tuddai da ruwan da ke tsakanin kasashe mambobin kungiyar ta NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.