Isa ga babban shafi

NATO za ta tura karin dakaru Kosovo bayan tsanantar arangama da masu bore

Dakarun wanzar da zaman lafiya sama da 30 na kungiyar tsaro ta NATO da aka tura zuwa birnin Kosovo sun jikkata, yayin arangama da wasu Sabiyawa da ke zanga-zangar neman a tsige magadan garin da aka zaba a baya bayan nan ‘yan asalin kasar Albania. 

Yadda ake arangama tsakanin masu zanga-zanga da dakarun wanzar da zaman lafiya na NATO.
Yadda ake arangama tsakanin masu zanga-zanga da dakarun wanzar da zaman lafiya na NATO. © REUTERS / LAURA HASANI
Talla

Tuni dai NATO ta tura karin dakarun wanzar da zaman lafiya cikin kasar ta Kosovo bayan arangamar ta jiya wadda shugaba Aleksandar Vucic na Serbia ke cewa ya kai ga kisan Sabiyawa 52.

Kungiyar tarayyar Turai ta bukaci kasashen na Serbia da Kosovo su yayyafawa rikicin ruwan sanyi bayan da Rasha ta yi zargin cewa kasashen yammacin Turai ke rura wutar rikicin wanda ke biyo bayan zaben magadan gari.

Sabiyawan Kosovo dai sunkauracewazaben da akagudanar a watan da ya gabata a garuruwanarewacinkasar, wanda ya baiwa 'yankabilar Albania damarmamayemukamanshugabancinkanananhukumomiduk da karancinkuri'un da akagani dakasa da kashi 3.5 cikindari. 

Ma’aikatar tsaron Hungary ta ce dakarun sojinta 20 na cikin wadanda suka jikkata a arangamar ta Kosovo, yayinda Firaministar Italiya Giorgia Meloni ke cewa dole har sai bangarorin biyu sun jaa da baya ne za a iya shawo kan rikicin tsakanin Servia da Kosovo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.