Isa ga babban shafi

Rikicin kabilanci ya barke a Arewacin Kosovo

Rikicin kabilanci ya barke a kasar Kosovo, inda ake fargabar mutane da dama sun rasa rayukan su, bayan da al’ummar Kabilar Serb ke adawa da nadin dan kabilar Albania a matsayin magajin garin yankin. 

Yadda jami'an tsaron Kosovo ke harba barkonon tsohuwa
Yadda jami'an tsaron Kosovo ke harba barkonon tsohuwa REUTERS/Marko Djurica
Talla

Kabilar Serb wanda sune marasa rinjaye sun janyewa zuwa kada kuri’a a zaben watan Aprilu da ya gabata, abinda ya baiwa Albaniyawan damar zaben dan Kabilar su, abinda kuma a yanzu Serbiyawan ke ganin ba zai yiwu ba. 

Tuni dai yan sanda suka fara harbi a sama da kuma jefa hayaki mai sa hawaye ga taron mutanen da ke rikici da juna, wanda ya haddasa rasa rayuka da kuma dukiyoyi. 

Tuni shugaban Serbia, Aleksandar Vucic ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a kan iyakar kasar da Kosovo, domin tunkarar rikicin da ka iya kunnowa kai daga yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.