Isa ga babban shafi

Hukumomi sun rufe kan iyakar Kosovo da Serbia saboda rikice-rikice

An rufe babbar hanyar kan iyakar Kosovo da Serbia a ranar Laraba yayin da aka kwashe watanni ana tafka rikici, lamarin da ya sa gwamnatin Washington da Brussels suka bukaci da a sassauta tashin hankalin cikin gaggawa.

Wani dan sandan kosovo kenan da ke tsaron kan hanya lokacin da shugaban Serbia ya kai ziyara kasar
Wani dan sandan kosovo kenan da ke tsaron kan hanya lokacin da shugaban Serbia ya kai ziyara kasar AP - Bojan Slavkovic
Talla

A shekara ta 2008 ne Kosovo ta ayyana ‘yancin kai daga Serbia, amma Belgrade ta ki amincewa da hakan tare da karfafawa Sabiyawan Kosovo 120,000 kwarin guiwa da su bijirewa dokar Pristina musamman a arewacin kasar inda al’ummar Serbia ke da rinjaye.

Rikicin baya-bayan nan ya barke ne a ranar 10 ga watan Disamba, lokacin da ‘yan kabilar Serbia suka kafa shingaye domin nuna rashin amincewarsu da kame wani tsohon dan sanda da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai wa jami'an 'yan sanda na Albania da ke da tasiri wajen dakile zirga-zirgar ababen hawa a kan iyakokin kasashen biyu.

Bayan da aka kafa shingayen, an kai wa 'yan sandan Kosovar da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa hari, yayin da sojojin Serbia suka kara kaimi a cikin wannan mako.

Da yammacin ranar Talata, masu zanga-zanga da dama a gefen iyakar Serbia suka yi amfani da manyan motoci da taraktoci wajen dakatar da zirga-zirga a kan hanyar zuwa Merdare, babbar mashigar da ke tsakanin kasashen makwabta, matakin da ya tilasta wa 'yan sandan Kosovo rufe hanyar shiga ranar Laraba.

Irin wannan kulle-kullen ba bisa ka'ida ba ya hana zirga-zirgar jama'a da kayayyaki cikin 'yanci, don haka muna gayyatar 'yan kasarmu da 'yan uwanmu da su yi amfani da wasu wuraren kan iyaka don yin zirga-zirga," in ji sanarwar 'yan sandan Kosovo.

Pristina ta kuma bukaci dakarun wanzar da zaman lafiya karkashin jagorancin NATO da su janye shingayen da aka kafa a kasar Kosovo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.