Isa ga babban shafi
EU-Balkans

EU ta ki bai wa kasashen Balkans damar zama mambobinta

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun ki amincewa da sanya wa’adin bai wa kasashen Balkans damar zama mambobin EU duk da matakin tabbatarwa kasashen shirin basu damar zama ‘ya’yan kungiyar a nan gaba.

Ursula von der Leyen yayin taron EU a Slovenia.
Ursula von der Leyen yayin taron EU a Slovenia. AP - Petr David Josek
Talla

Yayin taron da shugabannin na EU suka yi da shugabannin kasashen Balkans yau laraba, kungiyar ta Turai ta ce har yanzu ta na da kudirin bai wa kasashen damar zama mambobinta duk da jinkirin da aka samu wanda ya fusata su tare da sanya su kokarin sabunta kusancinsu da kasashen Rasha da China.

Sai dai duk da ikirarin na EU, har bayan kammala taron an gaza samun daidaituwa kan wa’adin da kasashen na Balkans za su jira gabanin zama mambobin kungiyar.

Kasashen na Balkans da suka kunshi Albania da Bosnia da Serbia da kuma Montenegro baya ga North Macedonia da Kosovo dukkaninsu na cikin nahiyar Turai a Taswira amma tsawon shekaru sun gaza samun damar zama mambobin EU yayinda su ke a baya ta fuskar ci gaba da tattalin arziki idan aka kwatanta su da takwarorinsu mambobin kungiyar.

Kungiyar ta EU dai ta gargadi kasashen na Balkans da yunkurin zamowa makusanta Rasha da China sakamon fushinsu na gaza samun damar zama mambobinta, tana mai cewa har yanzu suna da cikakkiyar damar zama mambobinta sai dai akwai bukatar lokaci.

EU ta sanar da shirin tallafin biliyoyin yuro ga kasashen na gabashin Turai yayin taron nasu da ya gudana a Slovenia inda Ursula von der Leyen ke cewa kungiyar na kallon kasashen a matsayin ‘yan uwanta da su ke da kusanci fiye da kowanne yanki a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.