Isa ga babban shafi
Kosovo

Kotun duniya ta tuhumi shugaban Kosovo da laifukan yaki

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta gabatar da tuhume-tuhume guda 10 akan shugaban kasar Kosovo, Hashim Thaci wadanda suka shafi aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin bil'adama a lokacin rikicin kasar a shekarar 1990.

Shugaban Kosovo Hashim Thaci.
Shugaban Kosovo Hashim Thaci. REUTERS/Hazir Reka
Talla

Masu gabatar da kara a kotun sun gabatar da zarge-zargen a ranar 24 ga watan Afrilu, amma sai a wannan lokacin aka bayyana su ga jama’a bayan watanni biyu.

Kotun ta ce, Thaci da Kadri Veseli da wasu abokan huldarsu na da hannu wajen kashe mutane a kalla 100 lokacin tashin hankalin, yayin da kuma ake tuhumar su da laifin batar wasu mutane da dama da azabtarwa.

Zargin ya shafi laifukan da aka yi wa daruruwan 'yan kasar Kosovo da Sabiyawa da Albaniyawa da kuma mutanen Roma.

Firaministan kasar mai barin gado, Ramush Haradinaj ya bayyana shirin sauka daga mukaminsa domin fuskantar shari’ar, wadda ta shafi kashe mutane kusan 13,000 akasarinsu 'yan Kabilar Albaniyawa lokacin rikicin.

Sakamakon wannan lamari, shugaba Thaci ya katse ziyarar da ya kai Amurka kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya rawaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.