Isa ga babban shafi

China ta yi gargadi kan shirin kulla kawancen NATO a yankin Asiya

Ministan tsaron kasar China ya yi gargadi game da kafa kawancen sojin kungiyar tsaro ta NATO a yankin Asiya da tekun Pasifik, yana mai cewa hakan zai jefa yankin cikin wani yanayi na rikici.

Ministan tsaron China Li Shangfu, yayin taron shangri-La, a Singapor 4/6/23
Ministan tsaron China Li Shangfu, yayin taron shangri-La, a Singapor 4/6/23 AFP - ROSLAN RAHMAN
Talla

Kalaman na Li Shangfu na zuwa ne kwana guda bayan da jiragen ruwan Amurka da na China suka kusanci juna a mashigin tekun Taiwan, lamarin da ya fusata bangarorin biyu.

Li ya shaida wa taron tsaro da aka gudanar a kasar Singapore wanda ya samu halartar sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin, ya ce Kokarin neman kafa kawancen kungiyar tsaro ta NATO a yankin Asiya da tekun Pasifik wani kokari ne na garkuwa da kasashen yankin da kuma wuce gona da iri.

Li bai ambaci sunan ko wace kasa ba, amma kalaman nasa sun yi daidai da sukar da China ta dade tana yi wa Amurka na neman kulla kawance a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.