Isa ga babban shafi

A karon farko NATO ta bayyana China a matsayin kalubale ga tsaronta

A karon farko kungiyar tsaro ta NATO ta bayyana China a matsayin babban kalubale ga tsaronta, tare da bayyana kusancin dake dada yin karfi tsakanin kasar ta Sin da Rasha a matsayin abinda ya sabawa manufofin kasashen yammacin Turai.

Shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO, yayin taron da suka gudanar a Madrid, babban birnin kasar Spain.
Shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO, yayin taron da suka gudanar a Madrid, babban birnin kasar Spain. REUTERS - POOL
Talla

Amurka ta dade tana matsa kaimi ga kawancen kasashen NATO kan su mayar da hankali sosai kan kasar Sin, duk kuwa da yadda wasu daga cikin kawayenta suka yi watsi da kiran.

Wata alama dake bayyana karin damuwa kan tasirin da China ke samu a duniya shi ne yadda a karon farko aka kawayen kasashen NATO, da suka hada da Japan, Korea ta Kudu, da Australia da kuma New Zealand suka halarci taron da kungiyar tsaron ta yi a Madrid, babban birnin kasar Spain.

Yayin da yake tsokaci kan kasar ta China, shugaban NATO Jens Stoltenberg ya nayar da misalin yadda kasar ke fadada karfin sojinta, ciki har da mallakar karin makaman nukiliya, da kuma cin zalin da take yi wa makwaftanta musamman kasar Taiwan.

Rabon da NATO ta yi gyara ga kundinta tun shekara ta 2010,  inda a bana, bayan kokawa kan tasirin China, kungiyar ta bayyana Rasha a matsayin barazana kai tsaye ga ‘ya’yanta biyo bayan mamaye Ukraine da ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.