Isa ga babban shafi

Amurka zata kara karfafa sojojin NATO ta kowane fanni a Turai - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da shirin karfafa sojojin Amurka dake NATO a nahiyar Turai, yana mai cewa ana bukatar kawancen adai-dai wannan lokaci fiye da  baya.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Amurka Joe Biden sun gaisa yayin da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg da Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson ke kallon taron zagaye na biyu a taron kungiyar tsaro ta NATO a Madrid, Spain, Yuni 29, 2022.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Amurka Joe Biden sun gaisa yayin da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg da Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson ke kallon taron zagaye na biyu a taron kungiyar tsaro ta NATO a Madrid, Spain, Yuni 29, 2022. REUTERS - POOL
Talla

Yayin taron wani taron ƙawancen ƙasashen Atlantika da ake gudanarwa a Madrid, shugaba Biden yace za’a karfafa NATO ta yadda zata kasance a kowane fanni – ƙasa da Sama da kuma ta ruwa.

Biden, wanda ke ganawa da Sakatare Janar na kungiayar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce zai yi karin dakarun kasar da su hada da:

Irin matakan da za'a dauka

- Haɓaka rundunar sojojin ruwan Amurka masu aikin wargazau dake Rota na kasar Spaine daga hudu zuwa shida.

- Kafa Hedikwatar Rundanar sojin dindindin ta biyar a Poland.

- "Ƙarin rundunar kai dauki a kasar Romania, wanda ya ƙunshi "dakaru 3,000 da kuma wata karin tawagar ma'aikata 2,000."

- Sake inganta dakarun sintiri a tekun ƙasashen Baltic.

- Karin wasu tawagogi biyu na jirgin F-35 na sirri zuwa Burtaniya.

- "Ƙarfafa tsaron sararin samani da sauran iyakokin Jamus da Italiya."

Tunkarar barazana

Da wannan mataki, shugaban Amurka Joe Biden yace tare da kawayen kasar za su tabbatar da cewa NATO a shirye ta ke wajen tunkarar barazanar daga ko wane bangare,"

Yayin da yake ishara da hadin kan kungiyar tsaro ta NATO kan amincewa da bukatar kasashen Finland da Sweden masu tsaka-tsaki a baya na shiga kawancen, Biden ya ce dabarun da Putin ya bi wajen mamaye Ukraine dara ce taci gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.