Isa ga babban shafi

Finland da Sweden sun kama hanyar shiga NATO bayan amincewar Turkiya

Shugaban kasar Finland Saulinii Niinisto ya ce a karshe dai Turkiyya ta amince da shigar kasashen Finland da Swedin cikin kungiyar tsaro ta NATO. Wannan dai na zuwa ne bayan gwagwarmayar da aka sha da shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan kafin amincewar sa.

Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg, Shugaban Turkiyya Recept Tayyip Erdogan da takwaransa na Finland Sauli Niinisto bayan sanya hannu kan takarda a Madrid, yayin taron NATO, Yuni 28, 2022
Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg, Shugaban Turkiyya Recept Tayyip Erdogan da takwaransa na Finland Sauli Niinisto bayan sanya hannu kan takarda a Madrid, yayin taron NATO, Yuni 28, 2022 © Yves Herman / Reuters
Talla

A cewar Boris Johnson kasashen Finland da Sweden sun kafa wani tarihi na zaman lafiya da zama ‘yan ba ruwan mu a don haka akwai bukatar su zama mambobin kungiyar ta NATO.

Sansanin NATO

Wannan dai na zuwa ne bayan da Jamus ta ce ta shirya tsaf don zama sansanin dakarun tsaro na NATO mafi girma a tarayyar Turai, wadanda zasu zama cikin shirin tunkarar Rasha a yakin da take yi da Ukraine.

A cewar shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, Jamus zata bi bayan gwamnatin Amurka wajen zama babban sansanin girke dakarun NATO.

Taron G7

A karin hasken da ya yi a yayin karkare taron kungiyar kasashen G7 Olaf Schols ya ce, daga watan Fabrairu lokacin da Russia ta fara Kutsa kai Ukraine Jamus ta kashe kudade har dala biliyan 100 don karfafa dakarun ta don shirin ko ta kwana.

Ko da yake mayar da martani kan zargin da ake yiwa Berlin din na nokewa wajen ware kudaden da ake ayyuka da su a kungiyar tsaro ta NATO, ya yi alkawarin ci gaba da biyan kudaden ba tare da jan kafa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.