Rasha da Ukraine na gab da cimma jituwar kawo karshen yakinsu - Turkiya
Turkiya ta ce kasashen Rasha da Ukraine na gab da cimma yarejejeniya a tsakaninsu da za ta kai ga kawo karshen mamayar da Kiev ke fuskanta daga Moscow.
Wallafawa ranar:
Ministan wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu ya ce duk da cewa abu ne mai wuya iya cimma daidaito tsakanin kasashen biyu ana tsaka da yaki, amma abin farin ciki ne yadda aka fara hango yiwuwar cimma jituwa.
A cewar Mevlut Cavusoglu bangarorin biyu na gab da cimma yarjejeniya kuma akwai alamun samun nasara, duk da yadda ake ci gaba da asarar rayukan fararen hula a Ukraine saboda hare-haren rASHA.
Ministan wajen na Turkiya ya ce yanzu haka kasar sa na kokarin shiga tsakani ciki har da shirin hada taro da zai gayyato shugaba Vladimir Putin da Volodymyr Zelensky na Ukraine don tattaunawar fahimtar juna.
Ankara da ke matsayin babban abokiya ga Moscow, ta karbi bakoncin ministocin wajen Rasha da Ukraine a Antalya duk dai a kokarin kawo karshen yakin kasashen biyu makwabtan juna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu