Isa ga babban shafi
NATO-Rasha-Ukraine

NATO ta sha alwashin ci gaba da bai wa Ukraine makamai babu shamaki

Kungiyar Tsaro ta NATO ta lashi takobin bai wa Ukraine tallafin makaman soji babu kakkautawa, a daidai lokacin da Finland ta jinjina wa kanta game da matakinta na shiga cikin kungiyar ta NATO.

shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky. © AP
Talla

Alkawarin na NATO na zuwa ne bayan Finland ta shafe gomman shekaru tana kin bada goyon baya wajen gina shingen tsaro a kan iyakar Rasha karkashin wani hadin-guiwa na ‘yan ba-ruwanmu, amma a yanzu ta sake salo, lamarin da ya bakanta ran gwamnatin Kremlin.

A bangare guda, Rasha ta sanar da kaddamar da hare-haren jiragen sama a gabashin Ukraine da kuma birnin Lviv da ke yammacin kasar a can kan iyaka da Poland.

A wani taron ministocin harkokin waje da ya gudana a birnin Berlin, Ministar Harkokin Wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce, za su samar da tallafin soji ga Ukraine muddin kasar na cikin bukatar haka domin kare kanta.

Shi ma Sakataren Kungiyar Tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce, Ukraine za ta iya samun galaba a wannan yakin, ganin yadda ‘yan kasar ke ci gaba da nuna jarumta wajen bai wa kasarsu kariya.

A yau Litinin ne ake sa ran ita ma Sweden za ta bi sahun Filand domin zama mamba a  kungiyar tsaron ta NATO duk kuwa da korafin da Turkiya ta yi na cewa, kasashen Sweden da Filand din na bai wa mayakan Kuradawa masu tsattsauran ra’ayi mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.