Isa ga babban shafi
NATO-Rasha

Ba mu da shirin girke dakaru a Ukraine don yakar Rasha- NATO

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya nanata cewa basu da shirin tura dakaru Ukraine, kalaman da ke zuwa bayan Poland ta mika bukatar ganin an girke dakarun wanzar da zaman lafiya.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, yayin jawabinsa gaban zaman tattaunawar ministocin tsaron kasashen kungiyar.
Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, yayin jawabinsa gaban zaman tattaunawar ministocin tsaron kasashen kungiyar. REUTERS - YVES HERMAN
Talla

A jawabinsa bayan taronsa da ministocin tsaron kasashen kungiyar, Stoltenberg ya bukaci shugaba Vladimir Putin na Rasha ya janye dakarunsa daga Ukraine yana mai cewa basu da shirin kai dakarunsu ta kowanne fanni don yakarsa.

Guda cikin bukatun Rasha kafin janye dakarunta daga Ukraine shi ne ganin Kiev ba ta shiga cikin kungiyar ta NATO ba, wanda kuma tuni Volodymyr Zelensky ya aminta da hakan.

Sai dai Zelensky ya yi watsi da tayin da Rasha ta yi na ganin Ukraine ta zama kasa ‘‘yar ba ruwana’’ idan har ta na bukatar a kawo karshen yakin na makwanni 3.

Shugaba Vladimir Putin ya nanata cewa ba zai janye daga Ukraine ba har sai ya cimma muradan da ya kaishi kasar ko dai ta fuskar yaki ko kuma ta Diflomasiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.