Isa ga babban shafi

Finland ta sanar da aniyar shiga kungiyar NATO a hukumance

Gwamnatin kasar Finland ta bayyana aniyarta ta shiga kungiyar tsaro ta NATO a hukumance, yayin da jam'iyya mai mulki a kasar Sweden ta gudanar da wani muhimmin taro da zai ba da damar shiga kungiyar ta NATO.

Fira Ministan Finland Sanna Marin da Shugaban Finland Sauli Niinisto sun halarci taron manema labarai na hadin gwiwa kan shawarar manufofin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Helsinki, Finland, 15 ga Mayu, 2022.
Fira Ministan Finland Sanna Marin da Shugaban Finland Sauli Niinisto sun halarci taron manema labarai na hadin gwiwa kan shawarar manufofin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Helsinki, Finland, 15 ga Mayu, 2022. © Heikki Saukkomaa/ Lehtikuva/via Reuters
Talla

Matakin na Finland ya zo ne kasa da watanni uku bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Akwai dai bukatar sai dukkanin mambobin kungiyar tsaro ta NATO 30 su amince da karbar Finland, kafin ta samu shiga cikinsu.

A karshen mako ne dai Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana rashin amincewarsa da shirin na Finland da Sweden dangane da shigarsu cikin NATO, amma shugaban kungiyar tsaron Jens Stoltenberg ya bayyana kwarin gwiwar shawo kan al’amarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.