Isa ga babban shafi
Macron-Finland

Macron ya goyi bayan Finland ta shiga NATO

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cikakken goyon bayan sa ga kasar Finland a yunkurin da take yi na shiga kungiyar NATO, bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine

 Emmanuel Macron, shugaban.
Emmanuel Macron, shugaban. © Ludovic Marin / Pool via REUTERS
Talla

Fadar shugaban kasar Faransa ta ce bayan tattaunawar da aka yi tsakanin shugaba Emmanuel Macron da takwaransa na Finland Sauli Niinisto ta waya, Macron ya bayyana goyan bayan ‘yancin kasar na zabin abin da take so.

Shugaba Niinisto ya ce shiga kungiyar NATO zai basu damar kare kan su ta fuskar tsaro, musamman wajen hulda da kasashen dake cikin kungiyar.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya yi alkawarin cewar zasu gaggauta nazari a kan bukatar na Finland, yayin da Majalisar dokokin Amurka da kasashen Jamus da Faransa suka ce duk suna goyan baya, kuma babu wata sarkakiyar da za’a samu dangane da amincewa da kasar a matsayin mamba.

Sai dai Rasha ta yi gargadin cewar za’a tilasta mata daukar matakan soji muddin Finland ta ci gaba da aniyar ta na shiga kungiyar, yayin da ta janyo hankalin shugabannin kasar a kan abin da ke iya biyo baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.