Isa ga babban shafi
Finland-Rasha-NATO

Finland za ta sanar da aniyar shiga NATO a hukumance

Ana sa ran gwamnatin Finland ta sanar da aniyarta ta shiga kungiyar tsaro ta NATO a  hukumance a yau Lahadi, a yayin da jam’iyya mai mulkin kasar Sweden  za ta gudanar da wani taro da  zai share fagen yiwuwar mika bukata ta hadin gwiwa da Finland.

Премьер-министр Финляндии Санна Марин
Премьер-министр Финляндии Санна Марин REUTERS - POOL
Talla

Kasa da watanni 3 da mamayar Ukraaine da Rasha ta yi, kasashen Finland da Sweden sun shirya don sauya manufofinsu na ‘yan ba ruwanmu’ da suka shafe shekaru 75 a Finland, da kuma sama da shekaru dari 2 Sweden.

kasashen 2 sun sassauta manufofinsu a kan akidar ‘ba ruwanmu’ ne a karshen yakin cacar baka ta wajen shiga kungiyar Tarayar Turai a cikin shekarun 1990s, lamarin da ya karfafa alakarsu da Turawan yamma.

Finland ce ke kan gaba  a wannan yunkuri na shiga NATO, a yayin da Sweden ke nuna daukin kasancewa kasar yankin tekun Baltic dayA tilo da ba ta cikin kungiyar tsaro ta NATO.

Sai dai ‘yan siyasan Sweden da dama sun bayyana cewa za su goyi bayan aniyar shiga NATO ne kawai idan Finland ta shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.