Isa ga babban shafi
Rasha - NATO

Rasha ta yi gargadi kan shirin Finland da Sweden na shiga NATO

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta yi gargadi kan makomar da za’a iya fuskanta idan kasashen Finland da Sweden su ka shiga kawancen tsaro na NATO da Amurka ke jagoranta, bayan da Moscow ta tura dakaru zuwa Ukraine.

Rundunar Sojan Sama da Makami mai linzami na Amurka suna tsaye kusa da baturin makami mai linzami na Patriot sama-da-yayin atisayen rukunin tsaro na kasa da kasa na NATO, Alhamis, 20 ga Yuli, 2017.
Rundunar Sojan Sama da Makami mai linzami na Amurka suna tsaye kusa da baturin makami mai linzami na Patriot sama-da-yayin atisayen rukunin tsaro na kasa da kasa na NATO, Alhamis, 20 ga Yuli, 2017. AP - Mindaugas Kulbis
Talla

A makon nan ne dai Finland ta ce za ta yanke shawarar ko za ta nemi shiga kungiyar ta NATO yayin da ita ma Sweden ke tattaunawa kan shiga kungiyar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce  zabin ya rataya ne ga mahukuntan kasashen Sweden da Finland. Amma ya kamata su fahimci illar da irin wannan mataki zai haifar ga alakar da ke tsakaninsu da kuma tsarin tsaron Turai baki daya.

Ta kara da cewa kasan cewar Sweden da Finland a cikin kungiyar tsaro ta NATO ba abu bane da zai ba da gudummawa wajen karfafa martabar su a idon duniya.

Tsohon shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev ya yi gargadin cewa Rasha za ta tura makaman kare dangi kusa da jihohi uku da ke kan iyakokin ta, idan Finland ko Sweden suka yanke shawarar shiga kungiyar NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.