Isa ga babban shafi
Ukraine - Rasha

Duniya ta harzuka saboda gano dimbim gawarwaki a yammacin Kyiv

Duniya na ci gaba da nuna fushinta a game da gano gawamman gawarwakin fararen hula a garin Bucha, kusa da birnin Kyiv na kasar Ukraine bayan janyewar dakarun Rasha daga yankin.

Wasu daga cikin gawarwakin da aka gano a garin Bucha na kusa da birnin Kyiv. Hukumomin Ukraine na zargin Rasha ne da kisan.
Wasu daga cikin gawarwakin da aka gano a garin Bucha na kusa da birnin Kyiv. Hukumomin Ukraine na zargin Rasha ne da kisan. AP - Rodrigo Abd
Talla

Wadanda suka ga gawarwakin sun ce wasu ma hannuwansu a daure aka kashe, lamarin da ya matukar tada hankula.

Birtaniya, Faransa Jamus da Amurka NATO da Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana alhini da bacin ransu bayan da suka samu rahotani a game da wannan kisa, da kuma hotunan kamfanin dilancin labaran faransa da ken una gawarwaki a warwatse a tituna.

Shugaban Faransa Emanuel Macron ya ce akwai alamu masu karfi da ken una cewa an aikata laifukan yaki, yana mai bayyana goyon bayan kiraye kirayen jagororin Tarayyar Turai da shugaban gwamnatin Jamus suka yin a karin takunkumai a kan Rasha.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi kira dakarun Rasha masu kisa, masu azabtarwa, masu fyade da barayi wadanda suka cancanci mutuwa bayan abin da suka aikata.

Shi ko Firaministan  Poland, Mateusz Morawiecki kira ya yi da a gudanar da bincike  na kasa da kasa a kan loamarin.

Babbar mai gabatar da kara ta Ukraine Iryna Venediktova ta ce gawarwakin fararen hula 410 ne aka gano a yankunan kewaye da Kyiv da aka ssake karbewa daga hannun dakarun Rasha.

Magaji garin Bucha Anatoly Fedoruk ya ce gawarwaki kusan 300 ne aka binne a wani wagegen kabari a kusa da wata majami’a.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta musanta wannan zargi, inda ta ce dakarunta ba su taba fararen hula ba, tana mai zargin Ukraine da yin luguden wuta a kan ‘yan kasarta, kana ta yada hotunan karya ad kafafen labaran kasashen yamacin Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.