Isa ga babban shafi
Ukraine-Rask

Dakarun Rasha sun fara janyewa daga yankunan arewacin Ukraine

A Asabar din nan Ukraine ta ce dakarun Rasha sun fara barin yankunan arewacin kasar a kusa da iyaka da babba birnin kasar Kyiv da birnin Chernigiv, a yayin da kungiyar agaji ta Red Cross suke wani shirin fara kwashe fararen huka daga birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa.

,Volodymyr Zelensky shugana kasar. Ukraine.
,Volodymyr Zelensky shugana kasar. Ukraine. AP
Talla

Ukraine ta ce dakarun Rash ana mayar da hankali ne a yankunan kudanci da arewacin kasar, kwana guda bayan da dubban mutane suka samu ficewa daga Mariupol da saurn yankuna a cikin ayarin motocin bas bas da sauran motoci.

Wani mai bai wa shugaban kasar Ukraine shawara Mykhaylo Podolyak ya ce Rasha ta mayar da hankali a kan wani sabon salo ne a mamayarta yanzu.

Ya ce a yayin da alamu ke nuna dakarun Rasha  na ficewa daga biranen Kyiv da Cherngiv, aniyarsu dai ita ce su karbe cikakken iko da yankunan da suka mamaye, don su zauna su kara karfi.

Podolyak ya ce lallai dakarun Ukraine za su bi su yanunan, su kuma kafa tsarin tsaron sama, kuma su kasance masu iko a wurin.

Mariupol ya kasance wani mahimmi birni na Ukraine  da ya sha luguden wuta daga Rasha, inda rhotanni ke cewa an kashe mazauna yankin dubu 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.