Isa ga babban shafi
Rasha - uKRAINE

Akwai fatan tattaunawar da Turkiya ke jagoranta ya sulhunta Rasha da Ukraine

Rasha ta baiyana cewar za ta sassauta yakin da ake gwabzawa a kewayen garuruwa biyu na Ukraine bayan tattaunawa da Ukraine a ranar Talata tare da nuna yiwuwar ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu. Sakamakon tattaunawar kai-tsaye da aka yi a fadar shugaban kasar Turkiya da ke Istanbul ya samar da kwanciyar hankali bayan shafe fiye da wata guda ana rikici da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da tilastawa miliyoyin mutane barin muhallan su.

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan yayin jawabi ga tawagar Rasha da Ukraine da ya karbi bakwanci don sasanta rikicin, 29/03/22.
Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan yayin jawabi ga tawagar Rasha da Ukraine da ya karbi bakwanci don sasanta rikicin, 29/03/22. AP
Talla

Burtaniya da Amurka sun nuna shakku kan kalaman na Rasha, amma dai Ukraine ta baiyana cewa mutane bakwai ne suka mutu sakamakon harin da Rasha ta aiwatar kan ginin gwamnati a birnin Mykolaiv.

Bayan tattaunawar, mai shiga tsakani na Ukraine David Arakhamia ya ce akwai isassun sharuddan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da shugaban Rasha Vladimir Putin za su cimma.

Sannan Arakhamia ya kuma yi kira da a samar da hanyar tabbatar da tsaro managarciya ta kasa da kasa inda kasashe masu bada tabbaci za su yi aiki dai dai da wata dokar NATO mai lamba biyar.

Hakanan, Mataimakin ministan tsaron kasar Rasha Alexander Fomin ya ce an samu nasara a tattaunawar da ake yi kan matsayin Ukraine na taka tsantsan a kan batun makamin Nukiliya

Bisa hakan ne, aka yanke shawarar rage fafatawar soji a kusa da babban birnin kasar Kyiv da kuma birnin Chernigiv, a cewar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.