Isa ga babban shafi
Ukraine - Rasha

Kusan 'yan Ukraine miliyan 4 sun tsere daga kasar sakamakon mamayar Rasha

Alkalumman majalisar dinkin duniya na nuni da cewa mutane miliyan 3 da dubu darin 8 ne suka tsere daga Ukraine tun da Rasha ta fara luguden wuta a kasar wata daya da ya wuce.

wasu 'yan gudun hijiran Ukraine a sansaninsu na kasar Poland.
wasu 'yan gudun hijiran Ukraine a sansaninsu na kasar Poland. Agencja Wyborcza.pl via REUTERS - Jakub Orzechowski/AGENCJA WYBORC
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta  majalisar, wadda ta ce an samu raguwar kwararar ‘yan gudun hijara, ta ce a Asabar, mutane dubu 48 da 450 suka bar kasar, kuma kimanin kashi 90 mata ne da yara.

Miliyan 2 da dubu dari 2 sun tsere ne zuwa makwafciya Poland, a yayin da fiye da rabin miliyan suka shiga kasar Romania, kana kusan dubu dari 3 sun samu sun shiga Rasha.

Kafin rikicin da aka fara wata daya da ya wuce, Poland, wadda mamba ce ta kungiyar tarayyar Turai, ta kasance gida ne ga kusan ‘yan Ukraine miliyan 1 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.