Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka-Ukraine

Biden zai ziyarci Poland don tattaunawa kan yakin Rasha a Ukraine

Shugaba Joe Biden na Amurka na shirin kai ziyara Poland a juma’a mai zuwa inda gana da shugaba Andrzej Duda don tattaunawa kan mamayar Rasha a Ukraine.

Shugaba Joe Biden na Amurka.
Shugaba Joe Biden na Amurka. REUTERS - ALEXANDER DRAGO
Talla

Fadar White House da ke sanar da wannan mataki ta ce Biden zai fara ganawa da shugabannin kasashe kawayen Amurka gabanin ziyarar zuwa Poland da ke da nufin samar da ayyukan jinkai ga ‘yan gudun hijirar Ukraine.

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin fadar White House Jen Psaki ta ce Biden zai gana shugabancin NATO da na G7 da kuma EU gabanin ziyarar a Poland, don tattauna yadda za su bullowa Rasha a abin da ya kira zaluncin da ta ke aikatawa a Ukraine.

Psaki ta ce za su ci gaba da jan hankalin Duniya don ganin sun ci gaba da samun goyon baya ga al’ummar Ukraine tare da sukar shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Sai dai Psaki ta ce ziyarar ta Biden ba ta da shirin kai shi zuwa Ukraine don ganewa idonsa yakin, sabanin shugabannin Poland da Czech da kuma Slovakia da suka je har Kyiv don ganewa idonsa yadda yakin ke gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.