Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka-Ukraine

Amurka ta sha alwashin hana Rasha nasara a yakinta kan Ukraine

Shugaba Joe Biden na Amurka ya sha alwashin hana takwaransa na Rasha Vladimir Putin samun nasara a yakin da ya kaddamar kan Ukraine dai dai lokacin da duniya ke caccakar jagoran na Moscow kan yadda sojojin ke sabbaba asarar rayukan dubban fararen hula.

Shugaba Joe Biden yayin jawabinsa kan tsauraran matakan da za su dauka kan Ukraine.
Shugaba Joe Biden yayin jawabinsa kan tsauraran matakan da za su dauka kan Ukraine. AP - Andrew Harnik
Talla

Biden yayin jawabinsa daga fadar White House ya caccaki shugaba Putin ya na mai dora masa laifi kan yadda ya haddasa samun ‘yan gudun hijira miliyan 2 a nahiyar Turai.

Acewar Biden zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin mamayar da Putin ke yiwa Ukraine ta zama asara amma ba riba ba ga Rasha.

Yayin jawabin Biden ya sanya haramcin fitar da man Rasha zuwa kasashen Duniya bayan da ya nanata cewa Amurka za ta tabbatar da kassara tattalin arzikin Moscow.

Joe Biden ya bayyana cewa tabbas Putin kwace birni amma ba zai iya ci gaba da rike Rasha ba.

Duk da takunkuman kasashen yammaci kan Putin, dakarun Rasha na ci gaba da dannakai sassan Ukraine a kokarin cimma muradun kasar na ganin ta kwace iko da wasu birane don kaucewa fuskantar illa kamar yadda shugaban ke ikirari.

Zuwa yanzu dai Rasha ta amince da aikin kwashe fararen hula daga biranen Ukraine 4 dai dai lokacin da yakin ya shiga kwana na 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.