Isa ga babban shafi
amurka - tsaro

Sojojin Amurka 4 sun mutu a Norway yayin atisayen NATO

Rundunar sojin Scandinavia ta sanar cewa wani jirgin sojin Amurka da ke atisaye cikin kungiyar tsaro ta NATO ya yi hatsari a kasar Norway, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dukkan sojojin Amurka hudu da ke cikinsa.

Wani Amurka dake aikin kungiyar tsaro NATO a Poland, 16/06/2017.
Wani Amurka dake aikin kungiyar tsaro NATO a Poland, 16/06/2017. AFP/File
Talla

Mutanen hudu dai na halartar atisayen sojan da ake yi na Cold Response wanda ya kunshi dakaru 30,000 daga kungiyar tsaro ta NATO da kuma kasashen kawance.

Kimanin jirage 200 da wasu jiragen ruwa 50 ne ke halartar atisayen, wanda za a ci gaba da gudanar shi har zuwa ranar 1 ga watan Afrilu.

Tun a yammacin ranar Jumma’a aka bada rahoton bacewar jirgin samfurin V-22B Osprey na rundunar sojojin ruwan Amurka a kudancin Bodo da ke arewacin Norway.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.