Dakarun Amurka da NATO sun fice daga sansani mafi girma a Afghanistan
Dukkanin dakarun Amurka da na kungiyar tsaro ta NATO sun fice daga sansanin sojin sama mafi girma dake Afghanistan a yau Juma’a, abinda ke tabbatar da janyewar dukkanin sojojin kasashen ketare daga kasar bayan shafe shekaru 20 suna gwabza yaki da kungiyoyin Taliban da Al Qa’eda.
Wallafawa ranar:
Sansanin sojin saman na Bagram dai ya kasance mafi muhimmanci ga dakarun na Amurka da na NATO a tsawon lokacin da suka shafe suna yaki da mayakan Al Qa’eda da Taliban tun daga shekarar 2001, bayan kai harin 11 ga watan Satumba a Amurka.
A ranar 11 ga watan Satumban dake tafe ake sa ran Amurka za ta Karkare janye dakarunta daga Afghanistan.
Cikin sanarwar da ta fitar ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce daga yanzu nauyin baiwa babban sansanin sojin na Bagram ya koma kan dakarun kasar, wadanda za su yi amfani da shi wajen karfafa yakin da suke na kokarin murkushe ta’addanci. Ita kuwa kungiyar Taliban bayan maraba da ficewar sojojin na Amurka da Nato cewa matakin dama ce ga ‘yan kasar Afghanistan ta fayyace makomarsu da kansu.
Masu sharhi kan lamurran tsaro na ganin nasarar sojojin Afghanistan wajen iko da sansanin sojin Bagram zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro a birnin Kabul da kewayensa, gami da samun nasara kan mayakan Taliban da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda.
A makwannin baya bayan nan, mayakan Taliban sun kame gwamman yankuna bayan kaddamar da hare-hare a wasu sassan Afghanistan, a yayin da su kuma dakarun kasar suka karfafa iko a manyan birane da sauran yankuna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu